Burina In Auri Shugaba Buhari… ‘Yar Wasan Hausa

Wata sabuwa inji Dan caca! Wata jarumar wasan Hausa, mai suna Fati Abubakar, wacce aka fi sani da fati Shu’uma ta ce bata da wani buri a duniya da ya wuce ta auri shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari.
“Wallahi Tallahi a rayuwata ban taba samun da namijin da ya shiga
raina, ya kwamta min a rai kuma nake masifar son shi sannan nake
burin auren shi, kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba,
sannan bani da buri da ya wuce na zama amaryar shi.”

Tace Shugaba Buhari Allah yayi masa da duk wata halitta da mace take bukata daga namiji Allah ya bawa Buhari wanda hakan ya sa take matukar ta ga ta aureshi wanda shine burinta a kullum.
Jarumar Wasan Hausa; Fati Shu’umaKalaman Jaruma Fati
Shu’uma kenan kamar yadda ta furta yayin wata ganawa da ita da
jaridar Blue Print ta yi a Kano, satin da ya gabata.
Shu’uma ta kara da cewar ‘duk inda ake neman namiji kyakykyawa
to shugaba Buhari ya kai, gashi fari dogo mai wushirya sannan
gajarumta, wallahi duk macen da ta auri Buhari tadace da miji,
kuma hakika na kamu da son shi fiye da duk wani da namiji a
duniyar nan, Allah ka sa in auri Buhari,” inji Fati.

Fati ta ci gaba da cewar “na san uwargidan shugaba Buhari Aisha,
kyakykyawar macece, amma duk da haka ina fatan karawa da ita
wajen mallake mijinta, sannan ina rokon dukkan ‘yan Nijeriya su tayani addu’a Allah ya cika min wannan burina nawa da
nake kwana da shi ina tashi, sannan Wanda keda halin sanar da
shugaba Buhari wannan buri nawa, don Allah ya taimaka min’.

Leave a comment