2019: Babu Sulhu Tsakanina Da Makiyan Jihar Kaduna – Inji El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa
babu sulhu a tsakaninsa da duk wasu yan siyasa da ta tabbata makiyan al’ummar jihar Kaduna ne,kamaryadda jaridar The Cables ta ruwaito.
Majiyarmu ta samu labain cewa El Rufai ya bayyana haka ne ta bakinmaimagana da yawuna, Samuel Aruwan,inda yace yana sane da cewa shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna na yunkurin harhada kan yan siyasan jihar.
Ya kara da cewa Gwamnan na goyon bayan wannan yunkuri, amma fa babu wanda zai sulhunta shi da yan siyasan da suka tabbatar da kansu a matsayin makiyan al’ummar jihar Kaduna.
“El-Rufai na sane da irin yunkurin da shugaban jam’iyyar APC Air Commodore Eammnuel Jekada ke yin a kokarin sulhunta sassan jam’iyyar APC da basa ga maciji a jihar, amma fa gwamna ba zai sulhunta da makiyan jihar Kaduna ba.” Inji shi. Daga cikin wadanda gwamnan ke da tsatstsamar dangantaka dasu akwai Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Lar, sauran sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar Hakim Baba Ahmed, Isa Ashiru da dai sauransu.

Leave a comment