2019: Ahmed Makarfi Shi Yafi Kowa Cancantar Zama Shugaban Kasa – Bashir Zubiru

An bayyana cewa tsohon gwamnan jihar kaduna Sanata Ahmed Mohamed Makarfi, shine yafi kowanne Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP cancantar shuhabancin Nijeriya a zaben shekarar 2019 Mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon shugaban majalisar dokokin jihar kaduna , Bashir Zubairu Birnin Gwari, yayin da yake gabatar da jawabin sa a gaban wakilan da zasu zabi Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Wanda aka gudanar da shi a kaduna.

Bashir Birnin Gwari, ya bayyana cewa bisa irin gudummawar da ci gaba da Makarfi ya kawo a jihar kaduna lokacin da yake gwamnan jihar da kuma yadda ya dawo da martabar jam’iyyar PDP bayan ta fadi zaben shekarar 2015, ya cancanci ya zama Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

A cewarsa duk Wanda ya san wanene Sanata Makarfi zai iya tabbatar da ingancin Makarfi a siyasar Nijeriya.

Yace lokaci yayi da duk wani Mai kishin jam’iyyar PDP da jihar kaduna da su tabbatar da sun zabi Makarfi a matsayin Dan takarar kujerar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP ranar 6 da 7 ga watan Oktobar wannan shekarar.

Haka kuma duk wakilan da zasu zabi ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, sun bayyana cewa kuri’ar su ta Makarfi ce, inda suka dauki alwashin cewa kuri’ar jihar kaduna ta Makarfi ce.

Taron Wanda ya samu halarcin tsohon mataimakin gwamnan jihar kaduna Ambasada Nuhu Audu Bajiga da shugaban marasa rinjaye Na majalisar dokokin jihar kaduna, Yakubu Bityon da da majalisar dokokin jihar kaduna Mai wakiltar mazabar karamar hukumar Kajuru da kuma shugaban karamar hukumar Zango Kataf .

Sauran sun hada da Alhaji Audi Yaro makama da tsoffin kwamishinoni da ‘yan majalisun jiha Dana tarayya lokacin da Makarfi ya ke gwamnan jihar kaduna, Da kuma daukacin wakilan da zasu zabi ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Leave a comment