HARKAR SIFURI: Gwamnatin Jihar Kaduna Zata Hada Hannu Da Kungiyar NURTW Da NATO

A kokarinta na inganta harkar sufuri, Gwamnatin jihar kaduna Zata hada hannu da kungiyar direbobi ta kasa NURTW reshen jihar kaduna da kungiyar masu motocin haya ta kasa NATO na jihar kaduna domin ganin an Kara bunksa harkar sufuri a jihar.

Shugabar hukumar sufuri ta jihar kaduna KASTRA Aisha sa’idu Bala, itace ta bayyana Haka a zantawarta da Wakilinmu a fadar gidan Gwamnatin jihar, Tana Mai cewa bisa irin gudummawar da kungiyayin suke bayarwa a bangaren sufuri, a fadin jihar, hakan ya sanya Gwamnatin jihar ta Zata hada hannu da su Wajen ganin an Kara inganta harkar sufuri, ta hanyar Samar da motocin haya irin na zamani Wanda hakan zai taimaka Wajen Kara bunksa hanyoyin samun kudadan shiga.

Aisha Bala, ta ce harkar sufuri Tana Samar da ayyukan Yi ga matasa da bunkasa hanyoyin samun kudadan shiga Wanda a cewarta , Gwamnatin jihar kaduna Tana da kyakkyawar shiri Na inganta harkar sufuri Wanda nan bada jimawa za’a aiwatar da tsare -tsare, Wanda kuma Al’ummar jihar zasu amfana da shi.

Aisha Bala, ta Kara da cewa, Yanzu Haka hukumarta Zata shirya wani taron masu ruwa da tsaki akan harkar sufuri a jihar kaduna domin lalubo hanyar da gwamnatin Zata tallafawa harkar sufuri.

Shugabar taci gaba da cewa, a kasashen da suka ci gaba, harkar sufuri Tana daga cikin bangaran da yake tallafawa ci gaban tattalin arzikin su, a cewarta, Gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai Zata tabbatar da cewa ta inganta harkar sufuri a jihar ya zama na zamani domin saukakawa Al’ummar jihar da kuma Samar da aikin Yi ga dimbin matasan jihar kaduna baki daya.

Leave a comment