ZABEN PDP: Saraki Ya Nemi Goyon Bayan Wakilan Jam’iyyar PDP Na Kaduna

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Abubakar Bukola Sarki, ya bayyana gamsuwarsa dangane da yadda wakilan jam’iyyar PDP da zasu zabi Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar suka tarba shi yayin da ya kawo ziyarar ganawa da jiga-jigan jam’iyyar da wakilan da zasu zabi Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a jihar kaduna.

Bukola Sarki, Wanda jam’iyyar ta shirya masa gagarumar tarba tun daga filin tashi da saukar jirage Na kaduna, ya bukaci goyon bayan wakilan da su zabi Dan takara a zaben fidda gwani da jam’iyyar zatayi a watan gobe, inda yace muddin suka zabe shi a matsayin Dan takarar kujerar shugaban kasa ba zai basu kunya ba, hasalima, zai dawo da martabar tattalin arzikin kasar da ya lalace a Yanzu.

Bukola Saraki, Wanda yana daga cikin masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar kujerar shugaban kasa, yace lokaci yayi da duk wani Mai kishin jam’iyyar PDP da kasa zai taimaka Wajen tunkude jam’iyyar APC daga kan shugabancin Nijeriya a zaben shekarar 2019.

Saraki, Wanda ya shigo sakatariyar jam’iyyar PDP bisa rakiyar Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Danjuma Lah da kuma Sanata Dino Melaye da sauran Manya ‘yan siyasa daga jihohi daban daban a fadin kasar nan.

Makida da mawaka da maroka duk ba’a barsu a baya ba Wajen baje kolin basirarsu domin tarbar Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Leave a comment