Tanko Almakura Da Abdullahi Adamu Sunyi Zaman Sulhu A Fadar Gwamnatin Nasarawa

Ana iya cewa rikita-rikitar siyasar jihar Nasarawa ta kawo karshe, biyo bayan zaman sulhu tsakanin gwamnan jihar Tanko Almakura da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Adamu.

Zaman sulhun Wanda ya gudana a fadan Gwamnatin jihar dake lafiya Babban Birnin jihar, Wanda suka kebanta kansu domin tattauna matsalolin siyasar jihar.

Abdullahi Adamu, Wanda ya shugabanci jihar Nasarawa sau biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya kuma zama Dan majalisar dattawan a shekarar 2007 zuwa Yanzu.

Sai dai zaman ba’a yarda manema labarai su shiga ba Amma majiyar mu ta shaida mana cewa zaman baya rasa nasaba da binciken kaf da gwamna Almakura ya sanya a yiwa tsohon gwamnan jihar Abdullahi Adamu na yin sama da fadi da wasu kudadan jihar, lamarin da ya Fara haifar da zazzafar siyasa a jihar.

Idan za’a iya tunawa kwanan baya gwamna Almakura ya Fitar da Dan takarar gwamna Wanda shima Abdullahi Adamu ya Fitar da nashi Wanda kuma Abdullahi Adamu ya jajirce sai Dan takarar shi ne zaiwa jam’iyyar APC takarar gwamna a jihar.

Hakazalika, Gwamna Tanko Almakura, yana yunkurin kwace kujerar Dan majalisar dattawan wato Abdullahi Adamu a zaben shekarar 2019, lamarin da sanya Gwamnatin jihar nasarawa ta umarci da ayi binciken kaf akan tsohon gwamnan, ko hakan zai sanya shi a janye hanun shi a batun Fitar da Dan takarar gwamna jihar.

Har ya zuwa lokacin kammala rubuta labarin babu sakamakon taron nasu

Leave a comment