Ministar Mata Aisha Alhassan Tayi Murabus

Ministar Ma’aikatar Lamuran mata, Aisha Alhasan , ta yi murabus daga kujerarta ta Minista.

Aisha Wacce akewa lakabi da maman Taraba, murabus din ta na zuwa ne bayan kwana biyu da jam’iyyar APC ta gaza tantance ta a cikin jerin masu neman tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin tutar jam’iyyar APC.
In za a iya tunawa, a bara ne Ministar ta fito a kafafen yada labarai, inda ta bayyana goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, inda ta ce har in zai fito takara, to lallai shi za ta zaba ba shugaban kasa Buhari ba.

Leave a comment