2019: Bama Fargabar Cin Zaben El-Rufai – Inji Abdu Kwari

Daraktan yakin neman zaben gwamnan jihar kaduna Alhaji Suleiman Abdu Kwari, ya bayyana cewa a zaben shekarar 2019 Mai zuwa basa Fargabar Dawowar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, kan kujerar gwamnan jihar, bisa yadda ya kawo ayyukan ci gaba a jihar.

Suleiman Abdu Kwarai, Wanda kuma shine kwamishinan ma’aikatan kudi Na jihar kaduna, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin zaben fidda gwani na gwamnan jihar, inda yace talakawan jihar sun tabbatar da cewa gwamna El-Rufai ya kawo musu ayyukan ci gaban jihar Wanda kuma babu shakka zasu kada masa kuru’un su idan zabe yazo.

Yace harkar ilimi da lafiya, Gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, ta taka rawar gani Wajen inganta bangaran yana Mai cewa babu wani gwamna a jihar da ya bayar da lokacin sa Wajen dawo da martabar jihar kaduna Kamar El-Rufai.

Kwari,wanda shima yana daga cikin masu takarar kujerar Dan majalisar dattawa daga shiyyar Arewacin jihar kaduna, yace Al’ummar jihar kaduna sun gamsu da Gwamnatin jihar bisa kokarinta na dawo da martabar jihar a idon duniya. Akan hakan ya bukaci daukacin Al’ummar jihar da su ci gaba da bawa Gwamnatin goyon bayan da suka kamata Wajen ganin ta cimma burin ta na kawo ayyukan ci gaban jihar baki daya.

Leave a comment