Yadda Uba Sani Ke Taimakon Al’umma – Inji MS Ustaz

A dai dai lokacin da zaben shekarar 2019 ke Kara karatowa, Al’ummar shiyyar kaduna ta tsakiya sun bayyana gamsuwarsu dangane da yadda Dan takarar kujerar Dan majalisar dattawa Wanda zai wakilci mazabar kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya, Malam Uba Sani, yake tallafawa rayuwar Al’ummar jihar.

Hakazalika sun bayyana Dakta Uba Sani a matsayin wani babban jigo a siyasar Jihar kaduna, dake kan gaba wajen taimakon Al’umma musamman marasa galihu dake fadin jihar kaduna da kewaye.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani Dan kasuwa kuma babban jigo a jam’iyyar APC dake Jihar kaduna, Muhammad Sani Abdulmajid, wanda aka fi sani da MS Ustaz, a yayin da yake ganawa da wasu tawagar ‘yan siyasa da ya kai masu ziyara a Karamar hukumar Cikun dake Jihar kaduna, domin bayyana masu irin manufofi da kudirin Dan takarar Sanata a kaduna ta tsakiya, Dakta Uba Sani.

MS Ustaz ya ci gaba da bayyana cewa, dalilin su na gani sun marawa Dakta Uba Sani baya domin ganin ya kai ga nasara a matsayin Sanata kaduna ta tsakiya shi ne, domin Uba Sani
mutum ne mai yawan taimakon Al’umma marasa galihu a ko da yaushe, wanda a kalla duk sati sai sama da marasa galihu dari 600, sun amfana da taimakon da yake bayarwa. Sannan kasancewa ta wanda muka shaku sosai, ina lura da yadda duk ranar juma’a, wannan Bawan Allah ke taimakon mabukata ta hanyar basu taimako batare da ya bari hannunsa na hagu ya sani ba. Sannan nakan ji shi yana yawan fadin cewa, a matsayinsa na Dan Adam, yana jin radadin yadda su ma marasa galihun suke ji, domin a cewarsa, duk wani Mutum mai imani dole ya tausayama na kasa da shi.

Muhammad Sani Abdulmajid, ya kara da bayyana ma ‘yan siyasar cewa, “abin da yake burge ni da wannan bawan Allah Uba Sani shi ne, yadda na tsinci wani katafaren Ginin Gida da wannan bawan Allah yake ginawa fisabilillah domin taimaka ma wasu marasa galihu, wanda a kiyasce a halin yanzu ginin ya lashe makudan kudade wajen naira dubu 375,000, kuma a halin yanzu ana kan gudanar da aikin kai tsaye ba tare da bata lokaci ba.”

Daga nan sai MS Ustaz, ya kara da rokon ‘yan siyasar da cewa lokaci yayi da zasu zabawar Al’umma shugabanni na gari irin Dakta Uba Sani, domin irin su ne kawai zasu taimaka ma Gwamnan Jihar kaduna da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, idan suka ce Majalisa.

Suma a nasu jawaban na godiya, sun godewa MS Ustaz a bisa jajircewarsa wajen yadda yake yada manufofin da kudurorin Dakta Uba Sani, a cewarsu tabbas kasancewar Dakta Uba Sani, tare da ‘yan siyasa masu kishin jama’arsu irin MS Ustaz, ba karamin nasara ba ne. Sannan sun nuna goyon bayansu dari bisa dari a kan tafiyar nasara irin ta Dakta Uba Sani.

Leave a comment