AGWOM ADARA: Kaduna Tayi Asarar  Jakadan Zaman Lafiya – Sarkin Koro

Sarkin Koro da ke cikin Karamar Hukumar Kagarko a jihar Kaduna Dakta Yohanna Akaito, ya bayyana mutuwar Agwom Adara Maiwada galadima, a Matsayin babbar asara ga al’ummar jihar kaduna baki daya.
Dakta Yohanna Akaito, Wanda aminin Marigayi Agwom Adara, ne yace jihar kaduna tayi Asarar Jakadan zaman lafiya Wanda mutuwarsa ta haifar da babban gibin da cike shi zaiyi wahalar gaske.
Sarkin Koro, ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da wakilinmu, inda yayi Allah wadai da wadanda suka kashe Marigayi Maiwada Galadima.
Dakta Akaito, yace, Marigayi Maiwada Galadima, ya bar duniya a dai dai Lokacin da jihar kaduna take  bukatarsa bisa burunsa na son zaman lafiya. 
Yace” Lokacin da na samu labarin mutuwar Marigayi sarki na kadu sosai ; na Shiga cikin dimuwa sosai, maganar Nan da mukeyi da Kai Ina yinta ne kawai saboda ni da Marigayi aminan juna ne , bashi da kamata banda kamarshi, gaskiya munyi Asarar dattijon arziki mai kaunar zaman lafiya” 
Akan Hakan Sarkin ya bukaci al’ummar jihar kaduna da su ci gaba da zama lafiya, acewarsa, babu Abin da yafi zaman lafiya muhimmancin ga rayuwar al’umma. ‎

Leave a comment