Zamu Kara Gina Ofisoshin ‘Yan Sanda A Yankunan Da Ake Samun Rikici – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, ya Dauki alwashin Kara Gina ofisoshin jami’an ‘yan sanda a wuraran da ake samun rikici a jihar Kaduna.
Gwamnan ya bada misali da kasuwar magani inda yace a binciken da sukayi kasuwar ta matse da yawa ta inda mutane basa samun cikakken walwala yayin cin kasuwar. Yace za ‘a gina babban Kasuwa inda za a bude hanyoyi ta inda koda ansami matsalar gobara masu kashe gobarar zasu samu damar shiga suyi aikinsu.
El-Rufai yace mafi yawancin rigingimun da ke faruwa barayi ke haddasa shi domin suyi anfani dashi wurin satar kayan mutane inda ya yi Kira ga mutane su basu cikakken hadin kai domin ganin ansamu zaman lafiya
El-rufa’i, yace za’a Kara samar da ofisoshin ‘yan sandan a unguwanni irinsu Narayi da Sabon Tasha da Badarawa da unguwar Yero Kasuwan Magani da dai sauransu Wanda Hakan zai taimaka wajen magance afkuwar rikicin Nan gaba

Leave a comment