RIKICIN KADUNA : Kungiyar Lauyoyi Ta Yaba Da Matakan Da Gwamna El-Rufa’i Ya Dauka

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa NBA reshen jihar kaduna, ta bayyana gamsuwarta dangane da Matakan da gwamnan jihar malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ya dauka na dakile yaduwar rikicin Kasuwar Magani Dana cikin Garin kaduna da.
Shugaban kungiyar Barista Sule Shu’aibu, shine ya bayyana Hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a kaduna, inda ya nuna takaicinsa dangane da yadda rikicin ya afku.
Kungiyar ta NBA, ta Dauki alwashin bayar da nata gudummawar na tabbatar da an hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen faruwar rikicin, inda tace ya zama wajibi a yaba wa gwamnan jihar da sauran hukumomin tsaro da suka bayar da gudummawar dakile yaduwar rikicin.
Hakazalika, Barista Sule Shu’aibu, ya Kuma bukaci gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin bincike Akan faruwar rikicin da Kuma kwamitin sulhu Wanda zai taimaka wajen magance afkuwar Hakan Nan gaba.
Kungiyar ta bukaci daukacin masu rike da sarautun gargajiya da malaman addinin kirista da musulmi da su ci gaba da nunawa mabiyansu muhimmancin zaman lafiya a fadin jihar baki daya.
Barista Sule Shu’aibu, yayi Kira ga daukacin al’ummar jihar kaduna da su ci gaba da zama lafiya Kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

Leave a comment