Bizi Mobile Da Hadin Gwiwar Masarautar Gwandu Sun Shirya Baje Kolin Hada-Hadar Kudi Na Zamani



Kamfanin Hada Hadar Kudi na zamani Mai suna  Bizi Mobile tare da hadin guiwar Kamfanin “MACCAT Agency Banking” karkashin jagoracin Masarautar Gwandu da Jihar Kebbi, sun shirya gudanar da gagarumin bikin baje kolin bankuna irinsa na biyu a tarihin Jihohin Arewa, wanda akayi ma lakabi da (2nd Agency Banking Fair Kebbi 2018) 
Shugaban rikunonin kamfanin Bizi Mobile  Aminu Aminu Bizi, ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, ya kara da bayyana cewa, kamfanin Bizi Mobile tare da hadin guiwar kamfanin MACCAT agency banking, karkashin jagorancin Masarautar Gwandu dake Jihar Kebbi, sun shirya tsab domin gudanar da bikin baje kolin bankuna da kamfanoni karo na biyu a tarihin Jihohin Arewa. Bikin baje kolin bankunan wanda a turance ake kira da 2d Agency banking Fair Kebbi 2018, zai gudana ne a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu dake Jihar Kebbi, daga ranar litinin 5/11/2018 zuwa Juma’a 9/11/2081. Tun daga misalin karfe 8 na safe zuwa 6 na yanma a kowa ne rana. Alhaji Aminu Bizi, ya kara da bayyana cewa, dalilin shirya wannan gagarumin taro wanda ake kira da baje kolin harkokin bankuna da kamfanoni, shi ne domin kusantar da su ga Al’umma. Ya ce, za’a gudanar da bikin baje kolin ne na tsawon kwanaki biyar, duk mai bukatar bude asusun ajiya za’ayi masa a nan take a wannan waje, kuma a bashi katin ATM nan take domin ya cire kudi a duk sadda yake da bukata. High Chief Aminu Bizi, ya kara da bayyana cewa, Kamfanin Bizi Mobile tare da hadin guiwar Babban bankin kasa da kuma bangarorin da suka shahara wajen tabbatar da ci gaban harkokin kudi, wanda tuni duniya ta ci gaba a wannan bangare. Wanda a dalilin haka kusan yanzu kamfanin Bizi Mobile ya karade duk Jihohin Nijeriya, ta fuskar Samar da hanyoyin masu sauki wajen mu’amula da kudade wanda tuni duniya ta wuce batun maganar rungumar kudi a jaka. Shugaban rukunonin kamfanin Bizi Mobile, ya yi kira ga daukacin bankuna, kamfanoni, manya da kuma kananan ‘yan kasuwa, har da Al’umma Gari baki daya, da cewa ga fa dama ta samu a gare su domin su zo su baje hajarsu kai tsaye wajen wannan gagarumin bikin baje koli irinsa na biyu a tarihin Arewa. Domin a cewarsa, ta wannan hanya ne kadai zasu sami damar zantawa da Al’umma kai tsaye ba tare da wani shamaki ba. Daga karshe ya yi kira ga daukacin Al’ummar Jihar Kebbi da sauran jihohi dake makwabtaka da jihar cewa, su fito kwansu da kwarkwartansu domin zuwa wajen gagarumin bikin baje kolin bankuna irinsa na biyu a tarihin Arewancin kasar nan, wanda aka yi ma lakabi da 2d Agency banking Fair Kebbi 2018, domin ganin sun zo domin bude asusun ajiya na bankuna, da kuma samun damar yin rijista domin zama agent na kowa ne banki kai tsaye, wato wakilin banki cikin Al’umma, wanda dama ne da babban bankin kasa wato CBN ya shimfida

Leave a comment