TSARO: Gwamnatin Kaduna ‎Zata Dauki ‘Yan Kato Da Gora Dubu 20 Aiki

A kokarinta na tabbatar da Tsaro a fadin jihar kaduna, gwamnatin jihar ta Dauki alwashin daukar matasa ‘yan sa Kai wadanda akafi sani da Kato Da Gora su Dubu 20 aikin samar da Tsaro a jihar.
Gwamnatin tace ‘Yan Kato ‎da Gora sun taka rawar gani wajen Hana rikicin da ya faru a jihar yaduwa, Wanda Hakan ya Sanya zata basu aikin samar da tsaro a jihar.
Gwamnan jiha malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ya sanar da Hakan a wani shirin gidan Radiyon Nigeria Kaduna Mai suna Hannu Da Yawa, inda yace bisa karancin jami’an Tsaro da jihar take Fama da shi Hakan ya Sanya gwamnatin zata basu aiki domin su taimakawa :yan Sanda da suke aiki a jihar kaduna. 
Gwamnan yace gwamnatin sa ta himmatu wajen tabbatar da samar da zaman lafiya. A fadin jihar Amma suna fuskantar matsalar karancin jami’an ‘yan Sanda a cewarsa, jihar kaduna tana Bukatar ‘yan Sanda guda Dubu 30 Amma yanzu wadanda suke jihar basu Kai guda Dubu 15 ba. Akan Hakan gwamnan ya Dauki alwashin Bawa ‘yan Kato da Gora Dubu 20 aikin samar da Tsaro a jihar.‎

Leave a comment