Uwargidar Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Shirin Wayar Da Kan  Mata Muhimmancin Shayar Da Jarirai Nonon Uwa

 

 Uwargidar Gwamnan Jihar Kaduna Hajiya Aisha Ummi El-Rufa’i, ta bayyana  muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shida tun daga haihuwa da cewa Yana Karawa Yara lafiya tun suna kanana da Kuma rage mutuwar su yayin da suke jirajirai.

Hajiya Ummi El-Rufa’i, ya bayyana Hakan ne yayin da take Kaddamar da shirin wayar da kan Iyaye mata ta kafafen Yada labarai da sada zumunta na zamani dangane da muhimmancin Shayar da jarirai Monon uwa Wanda ya gudana a Dakin taro na otel 17 da ke kaduna.

Uwargidar gwamnan ta Kaddamar da shirin ne a karkashin kungiyarta na tallafawa rayuwar Yara mai suna ” IMPROVE INFANT AND YOUNG CHILD FEEDING ” ‎, Wanda ya samu halarcin kungiyoyin lafiya na duniya Dana gida Nijeriya.

Hajiya Aisha Ummi El-Rufa’i, tayi nuni da cewa gudanar na nuni da cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla na watannin shidan farko shi ne abin da ya fi kome muhimmanci wajen ci gaban jaririn ta fuskar lafiya da kuma dorewar rayuwarsa.
‎.
Ta Kara da cewa  wayar da kan al’uma da ilmanatar da su da kuma kyautata koshin lafiyar iyaye mata na daga cikin matakan da ka iya taimakawa ga cimma burin shayar da jarirai nonon uwa a kasashe masu fuskantar koma baya a wannan fanni.

Mahalarta taron a jawabansu daban-daban sun bayyana cewa kashi goma sha uku cikin dari ne na jarirai a Nijeriya ke samun shayarwar nonon uwa zalla har ya zuwa watanni shidda na farkon rayuwarsu‎

Leave a comment