ZABEN 2019: Buhari Zai Samu Kuru’u Miliyan 15 Daga Arewa- Inji Isma’ila Ahmad

 

‎ Mataimaki na musamman ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari Akan shirin tallafawa al’umma, Alhaji Isma’ila Ahmed,‎ yace shiyyar Arewa suna da kuru’un da zasu kadawa Buhari sama da kuru’u Miliyan 15 daga cikin kuru’u Miliyan 20 da ake da su a shiyyar. 

Yace a Watan janairun wannan shekarar alkaluma daga hukumar zabe INEC ya nuna cewa akwai kuru Miliyan 20 daga Arewa Wanda yace babu tantama Buhari zai samu Miliyan 15 daga cikin adadin.

Ahmad, Wanda Yana daga cikin ‘yan kwamitin Yakin neman zaben Buhari a shekarar 2015, ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da manema labarai a kaduna Jim kadan Bayan kammala wani taron jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yammacin kasar Nan a hedikwatar jam’iyyar dake jihar kaduna. ‎

Alhaji Isma’ila Ahmad, yace duk da cewa zaben 2019 zai bambanta da sauran shekarun baya amma basa fargabar dawowar shugaban Kasa Muhammadu Buhari Akan karagar shugabancin kasar nana.

Yace tun Lokacin da Buhari ya hau karagar shugabancin kasar Nan tattalin arzikin kasar Nan ya bunkasa, matasa sun samu tallafi da Daman gaske.‎

Ya Kara da cewa gwamnatin Buhari tayi aiki amma bata da masu fadawa al’ummar kasar aikin da tayi inda ya roki ‘ya’yan jam’iyyar APC da su ci ga da Bawa gwamnatin goyon Bayan domin samun nasarar ta shekara 2019.‎

Akan Hakan, ya bukaci al’ummar kasar Nan da su ci gaba da Bawa gwamnatin Buhari goyon Bayan da suka kamata, inda yace abubuwa zasu sauya.‎

Leave a comment