Bama Fargabar Cin Zaben APC A Arewacin Kasar Nan- Shugaban Matasan APC Na Arewa


‎Shugaban Matasa na jam’iyyar APC na Shiyyar Arewa masu yamma Hon. Sadiq Fakai, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta kata rawar gani wajen rage matsalolin Cin hanci da rashawa da tsaro Wanda Hakan babbar ci gaba ne a siyasar kasar nan.

Yace magance matsalar cin hanci da rashawa ba karamar aiki bane a Kasa Kamar Nijeriya, cewarsa lokaci yayi da al’ummar kasar Nan musamman na shiyyar Arewa su Kara zaben gwamnatin Buhari a zaben 2019 Mai zuwa. 


Shugaban yace gwamnatin Buhari ta kawo abubuwan ci gaba a fadin kasar Nan, Wanda Hakan ya Sanya jam’iyyar ta gamsu da sahihancin shugaban Kasa Muhammadu Buhari. 

Yace Biyo Bayan irin ayyukan ci gaba da gwamnatin Buhari ta kawo a kasar Nan, basa Fargabar dawowar jam’iyyar APC Akan kujerun mulki a Matakai daban-daban a fadin kasar nan.‎

Akan Hakan, yace jam’iyyar APC na shiyyar ta Dauki alwashin ganin jam’iyyar ta lashe daukacin kujerun da suke shiyyar Arewa maso yammacin kasar Nan baki daya.‎

A nata jawabin Shugabar mata ta jam’iyyar APC na shiyyar Arewa Maso Yamma, Hajiya Yahanasu Buba, tace zasu tabbatar da arewacin kasar Nan jam’iyyar APC ta lashe zabe, inda tace Zasuyi bakin kokarinsu wajen tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta lashe daukacin kujerun da suke shiyyar.

‎Matasan sun bayyana haka ne a wani taron kaddamar da shugabannin masata na Yakin neman zaben shugaba Muhammadu buhari a zaben 2019, na  jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yammacin kasar Nan Wanda aka gudanar da shi a hedikwatar jam’iyyar na shiyya dake jihar kaduna.

Taron ya samu halarcin daukacin shugabannin matasa na jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma da kungiyoyin Yakin neman zaben shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a zaben 2019 Mai zuwa.

Leave a comment