Gwamnatin Kaduna Ta Amfana Da Naira Biliyan 13 Na Tallafawa Al’umma Daga Gwamnatin Tarayya- Ministar Kudi‎




Ministar Kudi ta Nijeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad, ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta amfana da duk shirye-shiryen tallafawa rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya.

Hajiya Zainab, ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter inda tace al’ummar jihar kaduna sun amfana da gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ministan ta ce gwamnatin Kaduna samu Kudi har naira biliyan 13.5 daga gwamnatin tarayya daga shirin ciyar da dalibai abinci Wanda aka kashe naira Miliyan daya a makarantu Dubu hudu a fadin jihar.

Hajiya zainab Shamsuna, tace gwamnatin tarayya ta kashe naira Miliyan 18 wajen horas da matasa 585 a shirin tallafawa rayuwar al’umma na  N-Power.

Tace duk wani shirin tallafawa al’umma da gwamnatin tarayya ta samar jihar kaduna tana amfana da shi ta kowanne bangare.‎

Leave a comment