Kotu Ta Yanke Wa Dan Majalisar Dokokin Jihar zamfara Hukuncin Daurin Shekaru 4 A Gidan Yari

Wata babbar kotu da ke zama a birnin Gusau na jihar Zamfara, ta yanke wa dan majalisar dokoki na jihar mai wakiltar mazabar Kauran-Namoda Lawali Attahiru Dogonkade hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, sakamakon samun shi da laifin damfarar kudin da ya  wan su ya kai Naira miliyan 31  .

Alkalin kotun mai shari’a Bello Shinkafi, ya yanke wa Dogonkade hukuncin ne a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan hukumar yaki da almundahana ICPC ta gurfanar da shi.

Hukumar ICPC dai, ta gurfanar da Dogonkade ne a kan tuhumomi hudu masu nasaba da damfara, kuma dan majalisar ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

Har ya zuwa lokacin da aka yanke masa wannan hukunci, Dogonkade ya kasance dan majalisar dokokin jihar Zamfara dake wakiltar mazabar Kauran-Namoda.

Dan majalisar ya yi amfani da matsayin sa ne wajen yin zambatar kudin sayen kayan aiki a asibitoci na sama da naira miliyan 31, laifin da ya saba wa sashe na 10 da 12 da 19 na kundin hukumar ICPC da aka kirkira a shekara ta 2000

Leave a comment