ZABEN 2019: Bani Da Fargabar Kara Lashe Zaben Kujerar Gwamnan Kaduna– EL-RUFA’I

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayar da tabbacin cewa a zaben shekarar  2019 Mai zuwa bashi da Fargabar Kara Cin Zaben sa a karo na biyu inda yace batu ne kamar anyi an gama duk da irin gwagwarmayar da ya yi cikin shekaru uku da rabi na ganin cewa ya yi abinda ya da ce a jihar‎.

Gwamnan ya jaddada Hakan ne  yayin da ya ke jawabi a taron majalisar koli na ma’aikatan Kudi ta tarayya  (NACOFED) Wanda aka gudanar da shi a Dakin taro na otel 17 dake jihar  Kaduna.
 El-Rufa’i  ya ce tsare-tsarensa ya fi muhimmanci a kan lashe zabe amma duk da haka yana ganin talakawa na tare da ‎
“Lashe zabe ba shine abinda muka sanya a gaba ba. Burin mu shine gudanar da ayyukan da suka dace domin gaskiya za tayi halinta a nan gaba.

“Duk da irin tsauraran matakan da muka dauke da wasu da ke fushi da mu, muna kyautata zaton cewa mu zamu lashe zaben 2019 a jihar Kaduna,‎
‎‎
Gwamnan ya Kara da cewa  gwamnatinsa ta yi garambawul a fanin ilimi, tattalin arziki da samar da lafiya kuma ana ganin amfanin hakan.‎

Ya ce abinda ya mayar da hankali a yanzu shine dora jihar akan turbar cigaba yayin da nasarori da cigaban da ya kawo a fanoni daban-daban na jihar za su zama hujja da zai sa al’umma su sake zaben shi.

El-Rufai ya ci gaba da cewa gwamnatinsa da kirkiri ayyuka da dama kuma ta tallafawa mata ta hanyar basu basusuka masu saukin biya kuma akwai niyyar cigaba da hakan.

Ya kuma ce jihar na shirin daukan ma’aikata a fanin lafiya fiye da 3000 domin inganta fanin samar da lafiya a jih

Leave a comment