Rikicin APC: Duk Wanda Ba’ayi Masa Adalci Ba Ya Garzaya Kotu – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce duk wanda aka yi wa ba daidai ba ko ya ke da korafi a kan zaben fidda-gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar ya garzaya kotu ya nemi hakkin sa.

Shugaba Buhari, ya bayyana cewa ba za su iya danne wa jama’a hakkin su ba, domin an kulla yarjejeniyar cewa za a gudanar da zaben fidda-gwani ta hanyar ‘yar tinke, ko kuma ta hanyar wakilan jam’iyya, ko kuma ta hanyar inda masu takara su ka cimma yarjejeniyar janye wa wani.

Don haka ya ce idan har wani ya na ganin an bi wata hanya ko wasu hanyoyin da ba daya daga cikin wadannan ukun ba aka danne hakkin sa na tsayawa takara, to zai iya zuwa kotu neman hakkin sa.

 

Leave a comment