Gwamnatin Tarayya , Jihohi Da  Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Biliyan 788 Na Watan Oktoba


A jiya Laraba ne Gwamnatin tarayya,  jihohi da Kananan Hukumomi na fadin kasar Nan  suka raba Kudi naira biliyan dari bakwai da tamanin da takwas da miliyan goma sha uku (N788,013,000,000) daga baitil malin kasa.‎
‎‎
Babban Akanta na Kasa Ahmad Idris, shi ya bayyana Hakan ga manema labarai a kaduna Jim kadan Bayan kammala wani taron koli na harkar Kudi da bunkasa tattalin arzikin Kasa Wanda aka gudanar da shi a Dakin Taro na otel 17 dake cikin Garin kaduna.
 Ahmad Idris,  yace an samu karin naira biliyan 89.42 daga kudin watan Satumbar data gabata.‎‎
‎ 
Ya ci gaba da cewa “Hukumar kasafta kudaden gwamnati ta bayyana cewar  kudi naira biliyan 682.16, wanda ya dara naira biliyan 569 da aka samu a watan Satumba da bambamcin naira biliyan 112.88.

“Haka zalika an samu karin sayar da gangan main a Najeriya da kusan ganga dubu dari takwas da ashirin, wanda hakan ya kara adadin kudin da aka samu zuwa dala miliyan hamsin da hudu fa dubu dari da casa’in, $54.19. sai dai farashin gangar mai ya fadi daga dala 75.69 zuwa dala 73.92‎
Taron ya samu halarcin daukacin kwamishinonin Kudi da Akantocin jihohi na jihohi 36 dake fadin kasar Nan da Kuma masu fada aji a harkokin Kudi da tattalin arziki daga sassan kasar Nan Wanda aka kwashe kwanaki uku Ana gudanar da shi.‎

Leave a comment