ZABEN 2019 : Ba Zamu Amince Da Magudin Zabe Ba- Atiku

Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, babu wata kafar tafka magudi a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabairu mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulda da jama’a ya fitar, Atiku ya shawarci Hukumar Zeban kasar, INEC da sojoji da jami’an ‘yan sanda da kada su bari a yi amfani da su wajen jirkita Demokradiya.

A cewar dan takarar na PDP, manyan kasashen duniya sun amince su yi amfani da tauraron dan adam na zamani wajen sanya ido kan zaben na watan gobe.

Atiku ya ce, jami’an gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na da masaniya game da tauraron dan adam din da za a yi amfani da shi a lokacin zaben, yayin da ya ce, mukarraban Buharin sun yi bakin cikin sanarwar da Amurka da Birtaniya da Kungiyar Kasashen Turai suka fitar game da dakatar da Walter Onnoghen daga kujerar Alkalin Alkalai.

Leave a comment