Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Maka Shugaba Buhari Kotu Kan Dakatar Da Alkalin Alkalan Kasar

 


Majalisar Dattawan Nijeriya ta garzaya zuwa kotun kolin kasar domin kalubalantar matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin kasar Walter Onnoghen.

A Wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki shawara kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu, wacce aka wallafa a shafin Twitter na ofishin shugaban majalisar, ta nuna cewa ana kalubalantar Buhari ne kan batutuwa biyu.

“Majalisar ta shigar da kara a kotun kolin ne domin ta nemi karin bayani kan ko matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin Najeriya, Walter Nkannu Onnoghen, ya saba dokar kasa,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Sannan majalisar har ila yau ta nemi kotun ta fayyace mata “ko matakin na shugaban na Najeriya ya shiga hurumin majalisar kamar sashi na 292 a kundin tsarin mulkin kasar,” ya nuna ita ce take da hurumin daukan wannan mataki.

Dalilin wannan kara da majalisar ta shigar, ya sa ta dauki matakin soke zaman da ta shirya yi a ranar Talata domin yin muhawara kan dakatar da Onnoghen a cewar sanarawar.

“An dage zaman majalisar da aka tsara za a yi a yau Talata

Leave a comment