‎‎ Babu Hannun Mu Wajen Maka Shugaba Buhari A Kotu- Ahmed Lawan.

Wasu Sanatocin Jam’iyyar APC da ke Majalisar Dattawan Nijeriya ya nesanta kansa da matakin da Majalisar ta dauka na maka shugaba Muhammadu Buhari a kotu saboda dakatar da alkalin alkalan kasar, Walter Onnoghen.

A Wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya sanya wa hannu, ta ce, babu hannun sanatocin na APC wajen daukan matakin shigar da karar Buhari a kotun.

Sanatocin na APC sun sanar da matsayarsa ne ga al’ummar kasar bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

A bangare guda kuma, Mai taimakawa shugaban Majalisar, Bukola Saraki ta fannin yada labara, Yusuph Olaniyonu ya fitar da wata sanarwa da ke cewa , Majalisar ta shigar da kara a kotun kolin kasar domin neman sanin halascin dakatarwar da Buhari ya yi wa Onnoghen.

Idan ba’a manta ba Shugaba Buhari ya dakatar da Onnoghen ne a ranar Juma’ar da ta gabata saboda zargin sa da bayar da bayanan karya kan kudaden da ya mallaka a asusunsa, abin da ya saba wa dokokin da kotun kula da da’ar ma’aikata ta kasar ta tanadar.

Sai dai suma Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa NBA sun nuna adawa da matakin dakatar da Onnoghen, in da suke cewa, shugaba Buhari ba shi da hurumin daukan irin wannan hukuncin a hannunsa.

NBA ta bukaci kotuna da su kaurace wa zama a ranakun Talata da Laraba a dukkanin fadin Najeriya domin zanga-zangar adawa da matakin.

Leave a comment