ZABEN 2019 : El-Rufa’i Ya Gargadi Masu Shirin Tada Rikici A Kudancin Kaduna

Gwamnan jihar kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ya gargadi masu shirin tada rikici yayin babban zaben  2019 da Kuma Bayan zaben a shiyyar kudancin jihar da su shiga taitayinsu inda yace gwamnati zata Sanya kafar wando da duk wani mai shirin kawo rikici a jihar.  

 Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta shirya daukar mataki Akan duk wani Wanda baya son zaman lafiya a jihar. 

Gwamna El-Rufa’i, ya bayyana haka ne a wani taro na masu ruwa da tsaki a karamar hukuma jama’a dake kudancin jihar a jiya inda yace tuni ya sanar da babban hafsan sojojin kasar nan Janar Tukur Buratai da babban hafsan tsaro na kasa  Abayomi Olanisakin da Kuma sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Abubakar Adamu Akan batun. 

‎ El-Rufa’i, ya kara da cewa ya samu rahoton sirri Akan cewa wasu mutane daga kudancin jihar suna shirin tada rikici Lokacin zabe da Kuma Bayan zaben Wanda daga Nan zai yadu zuwa sauran sassan jihar ta kaduna saboda sun samu Rahotannin cewa jam’iyyar APC zata Lashe Zaben Biyo Bayan yadda al’ummar jihar suka nuna kauna da goyon Bayan gwamnatin APC tun daga matakin tarayya zuwa jiha.‎ ‎ 

Acewar gwamnan tuni manyan jami’an Tsaron kasar suka bashi tabbacin turo jami’ansu domin kawo gudummawar kare rayukan al’ummar yankin. Akan Hakan, gwamnan ya bukaci Iyaye Da Su fadawa ‘ya’yan cewa katin zabe ne kadai zaizo wurin akwatin zabe yayin gudanar da babban zaben 2019 Mai zuwa

Leave a comment