Yan Bindiga Sun Kona ‘Yan Sanda Biyu Har Lahira A Jihar Katsina

Wasu ‘Yan Bindiga sun Kona akalla jami’an ‘yan  sanda biyu a karamar hukumar Hatsari dake jihar Katsina Bayan wata arangama da suka yi.‎

‘Yan sandan da aka kashe sune Sufeto  Bishir da Ibrahim sun rasa rayukansu  har lahira a wata arangama da aka yi tsakanin jami’an Tsaron ‘yan sanda a karamar hukumar Batsari da gungun wasu ‘yan bindiga da ake hasashen sun fi su 50 kowane dauke da manyan makamai.

Lamarin ya akfu ne a daren ranar Lahadi da misalin karfe 9pm a kauyen Shekewa yankin mazabar Magani duk a cikin karamar hukumar Batsari, inda yan bindigar suka cika garin suna ta harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Rahotanni sun shaida cewa  ‘yan sandan sun shigo kauyen ne domin kawo masu dauki daga babban ofishin ‘yan sanda na garin Batsari, inda yan bindigar suka zagaye su da harbi, har suka yi nasarar kone motar ‘yan sandan.‎

Leave a comment