MAJALISAR WAKILAI: Muna Goyon Bayan Hon. Nwajiuba Da Ya Zama Kakakin Majalisa- Yerima

A wani yunkuri na ganin Matasa sun dai daita salon siyasar kasar nan batare da nuna kabilanci ko bangaranci ba, kungiyar tuntuba ta Matasan Arewa, wanda a turance ake kira da Arewa Youth Consultative Forum(AYCF), karkashin jagoracin Alhaji Yerima Shettima, sun bayyana daukacin goyon bayansu ga Honarabul Chukwu Emeka Nwajiuba, a matsayin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Alhaji Yerima Shettima, ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a kaduna, a inda ya kara da bayyana cewa, sun yanke shawarar bayyana goyon bayansu ga dan yankin Kudu maso Gabas, ne saboda kowa ne dan yanki na da rawar da ya kamata ya taka a majalisa batare da nuna banbanci ba.

Shugaban na AYCF, ya qara da bayyana cewa, idan a na maganar cancanta ne, kaf duk cikin ‘yan takarar kujerar Shugabancin Majalisa, babu tamkar Honarabul Nwajiuba, domin yafi dukkaninsu cancanta saboda idan akayi la’akari da tsawon lokacin da ya xauka yana majalisa, sannan gashi kwararren a bangaren sasshe mulki da shari’a.

Alhaji Yerima Shettima, ya ci gaba da bayyana irin dimbin gudunmuwar da Honarabul Nwajiuba ya bayar tun lokacin da ya lashe zabe yazo majalisa, domin wakiltar Al’ummar mazabar Kudancin Ukigwe dake Jihar Imo, a Majalisar Wakilai ta Tarayya, tun daga shekarar 1999 zuwa 2003, wanda a lokacin shi ne Shugaban kwamitin Gidaje da Safiyo na majalisa, kamin daga bisani ya bar majalisa domin tsayawa takarar kujerar gwamna, wanda bai sami nasara ba.

A cewarsa, bayan zaman sa na kwararen lauya mai dauke da shaidar digirin na biyu, Honarabul Nwajiuba, na xaya daga cikin ‘yan kwamitin da su kayi aikin rubuta daftarin tsarin mulkin da ya kawo jam’iyyar APC a bisa mulkin kasar nan a halin yanzu.

Alhaji Yerima Shettima ya kara da bayyana cewa, daukacin Matasan Arewa na goyon bayan Honarabul Nwajiuba, saboda a matsayinsa na Matashin dan siyasa wanda bai da nuna banbancin kabilanci ko na addini, sannan gashi matashi wanda yake da kaifin basira da jajircewa wajen kishin Matasan kasar nan. Sannan a cewarsa, yana da tabbacin cewa har idan za’a tsaya ayi zaven gaskiya, to, ko shakka babu Honarabul Chukwu Emeka Nwajiuba, shi zai lashe kujerar Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya. A cewarsa.

Leave a comment