RAMADAN: Kungiyar JAP Ta Shirya Bude Baki Da Kungiyar Markatus Salafiyah A Zariya

Kungiyar ‘yan Jaridu Masu Ilimantar da iyaye akan Muhimmancin Rigakafin Shan-Inna (JAP) Reshen Jihar Kaduna ta shirya bude baki na musamman da kungiyar musulmai na Markatus Salafiyah.

Bude bakin wanda akayi a Masallacin Kungiyar dake kan titin Maje Tudun Wada Zariya a ranar lahadi da ta gabata, ya samu halartan Jama’a da dama.

Da yake jawabi Dakta Aminu Musa, wanda shine shugaban sashin kimiyyar Magunguna na jami’an Ahmadu Bello dake Zariya ya jawo hankalin iyaye akan su kula da kiwon lafiya na ‘ya’yasu ta hanyar kaisu asibi indai bukatan haka ya taso kuma su tabbata suna yarda ayi wa ‘ya’yansu rigakafi a kai-akai.

Dakta Aminu Musa, Ya jawo hankalin Iyaye akan su tabbata suna baiwa ‘ya’yan su abinci mai gina jiki kuma su kai rahoto abinda suka gani akan kiwon lafiyar ‘ya’yansu don ta haka dai taimaka wajen inganta kiwon lafiya na yara.

Dakta Aminu, wanda yake Magana akan kiwon lafiya a madadin kungiyar Sallafiya, ya shawarci jama’a akan cewa koshin lafiya na yara shine zai taimaka masu su cimma burin su na zama soja ko likita ko injiniya ko lauya da sauran ayyuka da dama in sun girma.

Yace haihuwan yara alfarma ne daga Allah don haka wajibi ne iyaye su kula da lafiyan su don su zama abun alfahari garesu da kuma kasa baki daya.

A nasa jawabin Babban Malami na Markatus Salafiyah, Malam Musa Sahabi ya godewa JAP saboda shirya wannan Bude Baki tare da addu’an Allah ya saka da Alhaii amin.

Har ilayau, Malam Musa ya yabawa Dakta Aminu Musa saboda bayanan da yayi akan fannin kiwon lafiyan yara, yace bayani ne na ilimi da sani.

Malam Musa ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya akan ta kula sosai da fannin tsaro, yace harkan tsaro a Nijeriya musamman a Arewa ya tabarbare.

Tunda farko, da yake nashi jawabin shugaban kungiyar yan jaridu masu ilimentar da iyaye akan muhimanci rigakafin Shan-Inna (JAP) reshen jihar Kaduna Alhaji Lawal Dogara, yace Kungiyar su ta shirya bude bakin ne don mu taya kan mu murnar wata mai Alfarma na Ramadan.

Har ilayau ya jawo hankalin Jama’a akan muhimanci Rigakafin Shan-Inna da sauran rigakafi da ake yiwa yara don su tashi da koshin lafiya.

Daga Shehu Yahaya,Kaduna

Leave a comment