Ba Zamu Ba Al’ummar Jihar Kaduna Kunya Ba- El-rufa’i

Gwamnan jihar Kasuna Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i, ya bayyana cewa gwamatin sa bazata ba lwa al’ummar jihar kunya ba ta hanyar ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba a karo na biyu na gwamnatinsa.

Gwamnan El-rufa’i ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar yayin rantsar da shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Gwamnan ya ci gaba da cewa “Nida mataimakiyata zamuyi iya bakin kokarinmu wajen kawo ci gaba a jihar Kaduna a wannan zango.
“Gwamnatin mu ta kowa da kowa ce Babu nuna bambanci saboda haka muna Kira ga daukacin al’ummar jihar Kaduna da su ci gaba da bamu goyon da ya kamata domin ganin mun kawo abubuwan ci gaban rayuwarsu Baki daya.
Da yake bayani dangane da ci gaban sha’anin tsaro a jihar da gwamnatinsa ta kawo, El-rufa’i yace “Mun kashe makudan kudade wajen magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar Kaduna ta Samar da kayan aiki ga jami’an tsaro a jihar. Haka zalika mun Samar da hukumar Samar da zaman lafiya Wanda burinmu shine Samar da dauwamammen zaman lafiya a fadin jihar Kaduna bakiya”inji
Gwamnan ya dauki lokaci yana zayyano ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a jihar a bangarori daban-daban, inda yace a bangaren harkar ilimi gwamnatinsa ta gina da inganta makarantaku firamare guda 4,200 a fadin jihar, acewarsa, gwamnatinsa ta mayar da ilimin firamare da karamar sakandare ga ‘ya’ya mata wajibi Wanda hakan yana daga cikin matakan da muka dauka na inganta sha’ainin ilimi a jihar Kaduna.
Akan hakan gwamnan ya bukaci alummar jihar Kaduna da su Bawa gwamatinsa goyon baya wajen tabbatar da an samu zaman lafiya da ci gaban jihar

Leave a comment