Uwargida Ta Cakawa Mijinta Wuka A Ciki A Jihar Kaduna

Rahotannin daga jihar Kaduna sun tabbatar da cewa mata mai suna Aisha ta nemi daukar ran Mijinta mai suna Yahaya Maiyaki ta hanyar caka mishi wuka a ciki.

A wani sako da kanin Mijin Alhaji Ahmed Maiyaki, ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace matar ta cakawa Mijinta wuka har sau uku a ciki Wanda yanzu yana asibiti ana bashi kulawa ta gaggawa.

Aisha, wanda suke zaune a layin Sardauna Cresent dake cikin karamar hukumar kaduna ta Atewa, ta cakamijin nata Yahaya A Maiyaki wukar da safiyar Juma’ar 25 ga watan Yulin 2019.

A ta bakin Maiyaki, yanzu haka Aisha Tana hannun jami’an tsaro.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana cewa tini ta tsuduma cikin bincike.

Leave a comment