Hukumar Kwastam A Shiyyar Neja/ Kogi Da Kwara Ta Tara Naira Biliyan 1.709, Ta Kwace Buhun Shinkafa 589

Hukumar Kwastan shiyyar Nija/Kogi/Kwara, ta ce ta tara Naira bilyan 1.709 Daga Watan Janairu zuwa Yulin wannan shekarar.
Da yake yi wa manema labarai bayani kwanturolan shiyya na hukumar, Yusuf Abba Kashim, ya ce, a bisa adadin kudin da hukumar ta tara, ya kai kashi 60 cikin 100 na yawan abin da ya kamata zuwa karshen wannan shekarar ta 2019 wato Naira biliyan 3,051,699,704.51
Ya kara da cewa sun kara inganta samun kudadan haraji a yankin inda a wata suna iya Tara naira miliyan 345,672,879 a wata Maris kadai, a cewarsa, a watan Mayu sun Tara naira 39,251,249.17.

A watan Juli sun Tara naira miliyan 227,994,063.91 sai watan Juli inda suka Tara naira miliyan 245,308,308.71
Abba Kassim, ya kuma bayyana cewa, hukumar na su ta kuma kwace buhunan shinkafa guda 589 wanda motoci guda uku suka yi fasa kwaurin su.

Shugaban, ya bugi kirjin hukumar na shi ta hana ‘yan fasakwari sakat a shiyyar tasu, ta hanyar kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin yankin.

Leave a comment