Gwamnatin Tarayya Ta Ware Dalar Amurka 200 Don Tallafawa Manoma

Gwamnatin Tarayya ta ware kudi Dalar Amurka Miliyan 200 domin tallafawa manoma kasar nan masu noman Masara da Citta da Kiwo Don samun Madara.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban shirin Bunkasa Aikin Gona Da Sarrafi shi da kuma Bunkasa rayuwar al’umma ta kasa wato “ AGRO- PROCESSING, PRODUCTIVITY ENHANCEMENT AND LIVELIHOOD IMPROVEMENT SUPPORT PROJECT ” a jihar Kaduna Dakta Yahaya Aminu Abdulahadi.
Dakta Yahaya Aminu, Wanda yake jawabi a taron bita da suka shiryawa Kungiyoyin manoma na shiyyar Arewacin Kaduna Wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Kongo dake Zariya.
Yace lokaci yayi da manema zasu koma yin noman Don samun riba maimakon noma Don cin abinci, Yana mai cewa akwai alfanu mai yawan gaske a cikin noman Masara Dana Citta da Kiwo Don samun Madara.

Shugaban Na (APPEALS), yace a binciken da aka gudanar ya nuna cewa a duk wata daya al’ummar karamar hukumar Zariya suna shan madara na naira miliyan daya da rabi, inda yace hakan babbar kuskure ne musamman ganin yadda madarar daga wata kasa ko jiha ake zuwa da shi.
Ya kara da cewa, ganin haka ya sanya gwamnati ta ware makudan kudade domin tallafawa manoma masu Kiwo Don samun Madara da masu noman Masara da Citta domin bunkasa sana’ar noman.
yace shirin zai taimakawa manoman domin jawo hankalinsu akan sanin alfanun da ke cikin Kiwo Don samun Madara da noman Masara Dana Citta inda yace akwai alheri mai yawa a cikin shirin.
Shirin na (APPEALS) Wanda hadin gwiwa ne da gwamnatin Tarayya da ta jihar Kaduna da kuma bankin duniya suka dauki nauyin gudanar da shi, an tanada shine ga masu Norman masara da Citta da kiwo domin samun Madara.

Dakta Yahaya Aminu, yace kungiyoyin manoma da matasa maza da mata da Nakasassu duk zasu amfana da shirin, Wanda hakan yana da cikin matakan da gwamnatin Tarayya da na jihar Kaduna suke dauka na bunkasa aikin gona a fadin kasar nan.
Da yake nasa jawabin, Darakta ma’aikatan gona ta jihar kaduna Mqlam Dauda Ashafa, yace Gwamnatin Buhari da ta El-Rufa’i sun bawa aikin gona muhimmanci Wanda hakan ya sanya aka Samar da wannan shiri na bunkasa aikin gona a fadin kasar nan baki daya.

Akan hakan, ya bukaci daukacin manoman da jihar da su shiga cikin wannan shirin tallafawa manoma masu noman Masara da Kiwo Don samun madara domin bunkasa sana’ar.
Shirin Wanda za’a ci gaba da gudanar da shi a fadin kasar nan har zuwa shekarar 2023 Mai zuwa, Wanda ake sanya ran cewa manoma a fadin kasar zasu fahimci yadda Ake Sarrafa kayan gona musamman Masara da Citta da Madara domin fadada hanyoyin samun shiga.

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment