Sana’ar Noma Tana  Rage Cin Hanci Da Rashawa- Dakta Yahaya Aminu

Shugaban shirin Bunkasa Aikin Gona Da Sarrafi shi da kuma Bunkasa rayuwar al’umma ta kasa wato “ AGRO- PROCESSING, PRODUCTIVITY ENHANCEMENT AND LIVELIHOOD IMPROVEMENT SUPPORT PROJECT ” a jihar Kaduna Dakta Yahaya Aminu Abdulahadi, ya bayar da tabbacin cewa sana’ar noma tana taimakawa wajen hana cin hanci da rashawa da barnatar da dukiyar al’ummar kasa.
Dakta Yahaya Aminu Abdulahadi, yace duk mutumin fa ya dukufa wajen sana’ar noma babu shakka zai kyamaci taba dukiyar al’ummar, inda yace aikin noma Yana da hanyoyin samun kudadan shuga masu yawan gaske.
Da yake jawabi a taron bita da shirin tallafawa manoma masu noman Masara Dana Citta da Kiwo Don samun Madara da bunkasa rayuwar al’ummar ( APPEALS) Wanda ya gudanar a dakin taro na Kango dake Zariya.
Akan hakan ya jawo hankalin shugabannin al’ummar da kungiyoyin manoma matasa mata da maza, da su fahimmaci cewa gwamnatin jihar Kaduna da ta Tarayya duk sunyi tanadi mai kyau wajen tallafawa aikin noma.
Shugaban ya ci gaba da cewa, duk Wanda ya dukufa wajen sana’ar noma babu shakka zaiyi adabo da fatara da talauci, hasalima, zai kyamaci cin dukiyar al’ummar kasa ta kowacce fuska.

Ya kara da cewa noman Masara Dana Citta da Kiwo Don samun Madara, akwai alfanu mai yawan gaske, duba da yadda al’ummar kasar na suke amfani da madara da ganyan shayi Wanda ake samu daga Citta da kuma yadda ake sarrafa Masara ta hanyoyi daban-daban.Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment