Gwamna El-Rufa’i Ya Kara Nada Wasu Mataimakansa

Biyo bayan Nada kwamishinoni da mataimaka gwamna da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i yayi a kwanan baya, a yau gwamnan ya kara Nada wasu karin mataimakasa a bangarori daban-daban.

A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanyawa hannu, yace gwamnan ya Nada masu taimaka masa ne domin ganin an samu ci gaba ta gangarori daban-daban a jihar.

Sanarwar tace gwamnan ya Nada mataimakan ne bayan zaman majalisar zartaswar jihar kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanada.

Wadanda aka Nada sun hada da Bulus Banquo Audu mataimaka a bangaren hukimar Tara bayanan filaye ta jihar (KADGIS) Da injiniya Musa Usman akan muhimman ayyuka da kuma Muhammad Mubarak, a kan aiwatar da manyan ayyykan jihar.

Sauran sunne mataimaki na mussamman a harkokin siyasa ,Mohammed Lawal Shehu da Darius Korau, akan siyasa da kuma Nay’marie Musa, akan harkokin siyasa sai kuma Aisha Hassan Dodo, a bangaren Tattalin arziki sai Umar Yahaya, mataimaki akan tsare-tsaren aiwatar da ayyuka a jihar.

Leave a comment