HAJJIN BANA: Anyi Jigilar  Muhajjata 2,710 Daga Jihar Kaduna Zuwa Kasa Mai Tsarki

A ci gaba da jigilar muhajjatan jihar Kaduna zuwa kasa mai tsariki a yau litinin jirgi na biyar ya kwashe muhajjatan jihar guda 529 zuwa kasar Saudi Arebiya.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar kaduna, Inusa Mohammed Makarfi, ya fitar yace wadanda aka kwashe yau sune jirgi na biyar mai dauke da mujjata maza guda 348 sai mata guda 181.
Inusa Makarfi, yace tun karfe takwas na safiyar yau litinin (Monday) muhajjatan suka isa filin jirgin masa na Kaduna.
Mujjatan wadanda aka tsara cewa ranar lahadi zasu bar jihar Kaduna zuwa kasa mai tsarki amma bisa wasu dalilan yanayi aka sauya zuwa litinin( Monday) yau kenan.
A zantawarsa da manema labarai, Mai kula da hukumar jin dadin alhazai na jihar Kaduna, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara,yace wannan tsaikon da aka samau ba zai haifar da matsala ba wajen jigilar muhajjatan lamarin da zai iya faruwa a ko da yau she.

Akan hakan hukumar ta bukaci daukacin muhajjatan da su kwantar da hankalinsu, inda ta dauki alwashin duk za’a kwashe su zuwa kasa mai tsarki cikin wannan makon.

Sanarwa tace mujjata guda 3,561 ake sanya ran zasu gudanar da aikin hajjin bana daga jihar Kaduna.

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment