Kungiyar Shi’a Tayi Watsi Da Hukuncin Haramtata

Kungiyar Yan uwa Musulmi IMN ta mabiya Shi’a a Nijeriya, tayi watsi da hukuncin wata kotun kasar da ya haramta ayyukanta, tare da bayyana ta a matsayin kungiyar Yan ta’adda.

Kungiyar ta nesanta kan ta daga ayyukan ta’addanci da kuma ayyuka masu alaka da haka, kamar yadda kotun ta bayyana.

Yayin zantawa da wani gidon radiyon kasar waje,mai magana da yawun kungiyar ta Yan uwa Muslmi Ibrahim Musa, ya ce suna da masaniya kan hukuncin kotun, sai dai zuwa lokacin da yake Karin bayanin, kungiyar ta Shi’a ba ta cimma matsaya kan martanin da za ta maida ba.

Malam Musa ya kuma jaddada yin watsi da zargin da gwamnati ke musu na aikata ta’addanci, da wasu ayyukan masu alaka da shi

Leave a comment