Kyautatawa Al’ummar Kaduna Shine Burinmu- Samuel Aruwan

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar kaduna Samuel Aruwan, ya bayyana cewa barin gwamnatin jihar shine kyautatwa rayuwar al’ummar jihar ta bangarori daban-daban.

Samuel Aruwan, wanda har ila yau shine kakakin gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, yace cikin shekaru hudu da saka gabata na shugabancin su, an samar da ayyukan ci gaban al’ummar kama daga samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata da kula da lafiya da bunkasa Ilimi da dai sauran, inda yace babu wani burin gwamnatin jihar da ya wuce kyautatawa rayuwar al’ummar jihar baki daya.

Aruwan, ya bayyana haka ne a wani shiri da gidan Rediyan Tarayya na Kaduna yayi dashi mai suna “Inda Babu Kasa” inda ya dauki lokaci mai tsawo yana bayyana irin masarorin da gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed el- rufai ta samu cikin shekaru hudu da suka gabata.

Kwamishinan, yace ofishinsa ya Dukufa wajen ganin an samar da tsaro a sassa daban-daban a fadin jihar, a cewarsa, sun fara daukar matakai domin magance matsalar rashin ya hanyoyin Birnin Gwari da kaduna zuwa Abuja, wanda yanzu al’amura sun fara yin sauki.

Da aka tambayeshi akan matakin da rundunar ‘yan sandar jihar kaduna ta dauka na dakatar sa ayyukan ‘yan kato da gora, Aruwan yace”Yanzu haka babu abin da zance amma nan gaba kadan zamu bayyana matsayarmu Akan batun”

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment