Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Dauki Alkalai Guda 40 Aiki

Biyo Bayan Karancin Alkalai a kotunan Majistare da suke cikin jihar Kaduna wanda hakan yake haifar da tafiyar hawainiya wajen yanke hukunci ga wadanda ake tuhuma da aikata laifu a jihar, gwamnatin jihar ta dauki Alkalai sama da guda 40 aiki domin kawo karshen tsaiko wajen yanke hukunci a katunan.

Kwamishinan ma’aikatar tsaro da Harkokin cikin gida na jihar kaduna, Samuel Aruwan, shi ya bayyana haka a wani shiri mai suna “Inda babu Kasa ” na gidan Rediyon Tarayya na kaduna yayi dashi, yace tuni Alkalan suka Kammala taron bita na kama aiki yanzu duk za’a rabasu zuwa kotunan da suka kamata domin fara aikin su.

Samuel Aruwan, ya kara da cewa daukar alkalan aiki zai taimaka wajen kawo karshen tsakon yanke hukunci ga mutanan sa ake tuhuma da aikata laifuka a kotunan majistare dake fadi jihar.

Ya bayyana kudirin gwamnatin jihar, na samar da guraben ayyukan yi ga matasa maza da mata a jihar, inda yace yanzu haka ma’aikatu daban- daban a jihar sun fara daukar aiki wanda a cewar sa, ya zuwa yanzu akwai matasa sama da guda dubu 25 da suka aiko da takardunsu na neman aiki.

Akan hakan, Aruwan ya bukaci daukacin al’ummar jihar kaduna da su ci gaba da bawa gwamnatin jihar goyon bayan da suka kamata domin ganin ta ci gaba da kawo abubuwan ci gaban su ta fannoni daban-daban.

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment