Sarkin Zazzau Zai Nada Sama’ila Suleman Dujiman Zazzau

Masarautar Zazzau ta kammala shiri domin nada dan majalisar wakilai a inuwar jam’iyyar APC mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Honarabul Sama’ila Suleman a matsayin Dujiman Zazzau.

Mai martaba sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris, ya tsaida ranar 15 ga watan satumbar wannan shekarar a matsayin ranar bikin nadin sarautar wanda zai gudana a fadar mai martaba sarki a birnin Zazzau.

Sama’ila Suleman shine na farko da masarautar Zazzau ta Nada a matsayin Dujiman Zazzau.

Masarautar Zazzau zata nada dan majalisar ne bisa jajircewarsa wajen tallafawa al’ummar mazabarsa ta bangarori daban-daban a zamansa wakili a majalisar Tarayya.

Honarabul Sama’ila Suleman, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya godewa Mai martaba sarkin Zazzau da karamcin da masarautar tayi masa.

Sama’ila Suleman, ya kasance dan majalisar wakili tun daga shekarar 2015 zuwa yau a zauren majalisar wakilai ta tarayya a in inuwar jam’iyyar APC.

Daga Shehu Yahaya, kaduna

Leave a comment