TSARO: Gwamnatin Nijeriya Ta Rufe Iyakokinta Da Kasar Nijar

Daga Shehu Yahaya, Maradi

A kokarin ganin an magance matsalar tsaro a Nijeriya, gwamnatin kasar ta rufe daukacin Kan iyakokinta da kasar Nijar.Rahotanni sun bayyana cewa kan Iyakokin zasu zama a rufe babu shiga babu fitan kaya da mutane har na tsawon wata daya.Wakilinmu da ya kai ziyara zuwa kan iyakokin Nijeriya da Nijar da ke Arewacin kasar, ya tarar da jami’an tsaro na hadin gwiwar ‘yan sanda da Soja da Kwastam ta ‘yan sandar farin kaya jimge sun hana kowa shigowa Nijeriya.Wasu jami’an kwastam da suka zanta da Wakilinmu wadanda suka bukaci a sakaya sunansu sun bayyana damuwarsu dangane da matakin da gwamnatin ta dauka na rufe kan Iyakokin wanda Hakan zai kara haifar da kuncin rayuwa a tsakanin al’ummar kasar Musamman masu karamin karfi.Akan Iyakar Babban Mutum da Kwangalam da Magama, Wakilinmu ya tarar da manyan Motoci dauke da kaya jibge, hasalima, mutane daga kasar Nijar dana Nijeriya masu shiga da fita a kafa da Kan babura duk sun tsaya cak.Wasu ‘yan kasuwa da suka zanta da Wakilinmu, sun bayyana rashin gamsuwarsu Akan matakin gwamnati na rufe daukacin Iyakokin inda suka bukaci mahukuntar kasar da su duba irin halin kuncin da al’umma Suke ciki ta bude kan Iyakokin.Sai dai a binciken TAURARUWA ta gudanar ya nuna cewa ofishin mai bawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkar tsaro suka bada umarnin rufe daukacin Iyakokin wanda a cewar, su hakan zai taimaka wajen lalubo hanyoyin magance matsalar rashin tsaro a kasar Musamman a Arewacin kasar inda yake fama da matsalar ‘yan ta’adda.Wakikinmu ya nemi jin ta bakin kakakin hukumar kwastam Attah, hakan yaci tura domin ya kirashi bai dauka ba.Hakazalika, Jami’an kwastam dake kan Iyakokin sun Kia Akan yadda aka hanasu Suyi aiki, inda jami’an tsaro na ‘yan sanda sune suka karbi ragamar kula da kan Iyakokin.

Leave a comment