TSARO : Malam Ahmed Abdulrahman Shine Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandar Jihar Inugu

Daga Nasiru Salisu

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana sunan Malam Ahmed Abdulrahman a matsayin sabon kwamishinan yan sandan jihar Inugu.

Malam Ahmed ya kasance tsohon Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna.

Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wasu gungun ‘yan bindiga sun kaddamar da hari a wani ofishin rundunar ‘Yan sandan dake Ikirike na jihar Inugu.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga ofishin ‘Yan sandan ne kamar za su kai musu kara, amma shigarsu ke da wuya, sai yan bindigan suka bude musu wuta.

Sai dai babu tabbacin ko akwai wanda aka kashe a sanadiyyar wannan harin, haka zalika babu tabbacin ko sun kwashe makaman dakunan.

Kakakin rundunar Yan sandan jihar Inugu, Ebere Amaraizu ya tabbatar da kai harin, amma yace babu wani mutu ko daya da aka kashe, amma yace sun kaddamar da farautar miyagun don hukuntasu.

Leave a comment