NULGE Ta Yaba Wa Gwamna El-Rufai Kan Sabon Albashi

Daga Shehu Yahaya, Kaduna
Kungiyar Ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE reshen jihar Kaduna ta jinjinawa matakin da Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmed el-rufai ya yanke na fara wanzar da biyan albashi mafi karanci ga kanan ma’aikatan gwamnati dake jihar ta Kaduna a cikin watan Satumbar da za’ a shiga.

Shugaban rikon kwarya na kungiyar ta NULGE reshen jihar Kaduna Kwamarade Rayanu Isyaku Turunku ne ya yi wannan yabon ga Gwamna Malam Nasir el-rufai a cikin sanarwar da ya sanya hannu

Kwamarade Rayanu Isyaku Turunku ya kuma sanar da cewa, wannan matakin na gwamnatin Gwamna Malam Nasir Ahmed el-rufai zai taimaka matuka wajen ragewa daukacin kananan ma’aikatan jihar, nusamman ma’aikatan kananan hukumomin dake a cikin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna saukin rayuwa.

Mai rikon kwaryar kungiyar ta NULGE reshen jihar Kaduna Kwamarade Rayanu Isyaku Turunku ya kuma yabawa.

Gwamna Malam Nasir Ahmed el-Rufai wajen kasancewar sa gwamna na farko daga cikin takwarorin sa na yin wannan babban matakin na yinkurin fara biyan sabon mafi karancin albashin na kananan ma’aikatan jihar da gwamnatin sa zata fara wanzarwa a watan Satumbar wannan shekarar ta 2019.

A cewar Shugaban na rikon kwarya na kungiyar ta NULGE Kwamarade Turunku, wannan matakin na Gwamna Malam Nasir Ahmed el-rufai ya nuna cewar ya damu matuka don inganta rayuwar kananan ma’aikatan dake a daukacin fadin jihar, musamman kananan ma’aikatan dake a kananan hukumomi 23 dake a daukacin fadin jihar.

A karshe, Shugaban rikon kwarya na kungiyar ta NULGE Kwamarade Rayanu Turunku ya kuma kara baiwa gwamnatin jihar da kuma tare da kungiyar tabbacin cewar, ma’aikatan na kananan hukumomin dake jihar, zasu kara zagewa wajen yin aiki tukuru da kuma baiwa gwamnatin jihar goyon bayan su don kara ciyar da jihar gaba da kuma cimma nasarar muradun da gwamnatin jihar ta sanya a gabaKungiyar Ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE reshen jihar Kaduna ta jinjinawa matakin da Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmed el-rufai ya yanke na fara wanzar da biyan albashi mafi karanci ga kanan ma’aikatan gwamnati dake jihar ta Kaduna a cikin watan Satumbar da za’ a shiga.

Leave a comment