Saboda Ayyukan Batagari Muka Rufe Iyakokin Nijeriya- Buhari

Daga Nasiru Salisu, Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dalilan da ya sanya Nijeriya ta rufe kan Iyakokin ta na wucin gadi da kasar Nijar da Benin shi ne saboda ayyukan wadansu bata gari suna safarar shigo da shinkafa ta barauniyyar hanya duk da haramtawa da kasar ta yi.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar inda ya tabbatar da cewa; shugaban kasar na ci gaba da nuna damuwa na yadda ake shigo da shinkafa ta barauniyyar hanya cikin Nijeriya

Shugaban kasar ya bayyana dalilai ne a taron da yake ci gaba da gudana domin bunkasa nahiyar Afrika a birnin Yokohama na kasar Japan a ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa; an rufe iyakar Seme ne tun bayan umurnin da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe iyakar na wucin gadi, inda aka kai dimbin jami’an tsaro domin bai wa iyakar tsaro na musamman. Shirin wanda aka yi take da ‘Ex-Swift Response’, ya hada jami’an Kwastam, hukumar lura da shige da fice, jami’an tsaron ‘yan sanda da na soji da hukumomin tsaro na farin kaya wanda ofishin bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro ke jagoranta.

Leave a comment