Hukumar Hisbah Zata Samar Da Makarantar Horas Da Jami’anta A Kano

Daga Nasiru Salisu, Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta samar da makarantar da za ta rika horas da jami’anta dake dukkanin fadin jihar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ya bayyana, inda ya ce; mukaddashin babban Daraktan hukumar, Dk. Aliyu Musa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a garin Kano.

Inda yake cewa; “dukkanin jami’an Hisbah a jihar Kano akwai bukatar su rika bayyana kyakkyawan mu’amala ga dukkanin al’umma. Wannan yana daya daga cikin babban aikin Hisbah, wato zama kyakkyawan misali domin tabbatar da an bi doka da oda.” In ji sanarwar.

Sun kara da cewa; ba za su gajiya ba wajen ci gaba da yakar miyagun ayyuka daga al’umma. Musa ya ci gaba da cewa; hukumar ba za ta amince da zuwa wurin aiki a latti ba, da kuma kasala a aiki da rashin da’a, inda ta tabbatar da cewa; duk wanda ta kama da daya daga cikin wannan halin, za ta hukunta shi.

Leave a comment