TSARO: Gwamnatin Kaduna Ta Gindayawa ‘Yan Kato Da Gora Sharruda

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Gwamnatin jihar kaduna ta bayyana cewa muddin masu aikin sa kai Akan Harkokin tsaro a jihar wadanda akafi sani da “‘Yan Kato Da Gora” suna bukatar ci gaba da gudanar da ayyukan su a jihar, sai sun bi sabbin dokokin da ta gindaya musu.

Gwamnatin tace ya zama wajibi ga duk wani mai sha’awar yin aikin sa kai Akan harkar tsaro sai yayi rijista da hukumar ‘yan sintiri na jihar wato “Kaduna Vigilant Service” wacce aka kafa domin kula da ayyukan tsaro na sa kai, haka kuma ba’a yarda da su rika yawo da madame tsirara a cikin unguwa , tare da hukunta masu laifi ba.

Kwamishinan ma’aikatar tsaro da Harkokin cikin gida na jihar kaduna Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da gidan Radiyon tarayya na kaduna yayi da shi, inda yace aikin samar da tsaro ba aiki bane na kara zube ; aiki ne wanda yake bukatar nazari da bin ka’idoji, Wanda hakan ya sanya suke shawartar duk mai son bada gudummawa Akan aikin sa kai na tsaro yabi sabbin dokokin da gwamnatin ta gindaya in kuma ya saba, babu shakka za’a hukuntashi.

A makon da ya gabata ne Rundunar ‘yan sandar jihar kaduna ta bayar da umarnin dakatar da ayyukan ‘Yan kato da Gora a jihar, Lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar.

Samuel Aruwan, ya ci gaba da cewa “Ba zamu aminta da wasu su rika yawo da bindiga ko makami ba a cikin unguwa ko kuma a bude wurin ajiye masu laifi ba, Alhali shi ba jami’an tsaro na gwamnati bane, saboda haka duk masu son yin aikin sa kai na samar da tsaro a jihar Kaduna suje suyi rijista da hukumar ‘yan sintir na jihar domin tantance su kamin su fara aikin, duk wanda ya kauce yin hakan babu shakka zai fuskanci fushin hukuma” in inji shi.

Kungiyar ‘yan kato da Gora sun bayar da gagarumar gudummawa wajen kwantar da rikici a jihar kaduna lokacin da wasu ‘yan ta’adda suka kashe wani basarake a jihar, wanda ya haifar da rikicin addani a wasu sassa na jihar.

A wancan lokacin gwamnatin jihar ta jinjinawa ‘yan kato da Gora bisa rawar da suka taka na tallafawa gwamnatin wajen samar da tsaro.

Rahotanni sun ruwaito cewa kungiyar ‘yan kato da Gora ta fara wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukanta Musamman ganin yadda suke hukunta masu laifi a cikin unguwa ba tare da yin bincike ba, hasalima, ana zarginsu da sanya masu laifi cikin mambobin kungiyar wanda hakan ya sanya aka gindaya musu Sabbin dokoki.

Leave a comment