LALATA DA DALIBA: Kotu  Ta Tasa Keyar Malamin Kwalejin Kimiyya Da Fasaha  Ta Jihar Kano Gida Yari

Daga Shehu Yahaya, Kano
Wata Kotun Majistare dake zamanta a jihar Kano ta bayar da umarnin ci gaba da garkame Wani Malamin Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta jihar (Kano Polytechnic ) Mai suna Shehu a gidan Yari.
Kotun Tana Tuhumar Shehu ne bisa zarginsa da yin lalata da Dalibarsa dake karatu a kwalejin.
Kotun Dake zamanta a Kan Titi Zungeru dake Karamar hukumar Fagge a jihar Kano, tace Ana zargin Shehu da laifin cin amana da Lalata da Daliba, wanda ya saba doka mai lamba 95 da 98 ta Final Kod.
Badamasi Gawuna, shine dan sanda mai gabatar da kara, ya shaidawa Alkalin kotun mai shari’a Muhammad Idris, cewa an damke malamin kwalejin ne yayin da hukumar Karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano ( Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission (PCACC) ta gudanar da wani bincike akan Korafin da aka kawo mata akan Shehu yana lalata da ‘yan mata Dalibai.
Gawuna yace Shehu ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Agustan wannan shekarar Kano.
Yace a wannan ranar da Misalin karfe 11 na safe wanda ake tuhuma da laifin ya dauki dalibar wacce Aka bukaci a sakaya sunanta zuwa wani Kanti mai suna Ummi Plaza da ke Kano domin ta taimaka mishi wajen rubuta sakamakon jarabawar Dalibai da sukayi na karshen zangon karatunsu.
Gawuna ya ci gaba da cewa, suna zaune tana taya shi (Shehu) aiki, kwastam bata Ankara ba sai ya fara tura hannunshi a cikin Farjinta da karfi.
Doka Kotun ta tambayi Wanda ake tuhuma Akan laifin, ya tabbatar da aikata laifin Inda alkalin kotun dris ya bada umarnin ci gaba da garkame Shehu a gidan yari har sai ranar 15 ga watan Oktobar 2019 domin ci gaba da sauraron karar.

Leave a comment