SACE YARAN KANO: Kungiyoyi Sunyi Zanga-Zanga A Kano

Daga Nasiru Salisu, kano

Gamayyar Kunigiyo masu zaman kansu a jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana yau domin nuna takicinsu kan yadda yan jaridu suka yi shiriu da batun yaran da aka sace a ka kai jihar Anambra aka kuma mayar da su kirista.

Gamayyar kungiyoyin sun yi tattakin ne yau a nan Kano inda suke dauke da rubutu da ke nuna yin Alawadai da al’amarin tare da zarigin yan jaridu da kuma gwamnati da yin guma da bakin su.

Guda daga cikin masu zanga-zangar Shazali Abubakar Adamu ya shaidawa freedom Radio cewar sun fito zanga-zangar ne domin nuna adawa da satar yaran aka kuma mayar da su kirista, amma gwamnatoci suka yi shiru.

Satar yaran Kano da munafurcin kafafan yada labarai
Yaran Kano: Majalisar dokokin Kano zata dauki mataki
An siyar da ‘ya ta naira Miliyan Daya da rabi

Leave a comment