Ina Da Samari Sama Da Biliyan Daya- Aisha Tsamiya

Daga Nasiru Salisu,Kano

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Aisha Aliyu Tsamiya, ta ce tana da samaruka wadanda suke sonta sama da biliyan daya.

Aisha Tsamiya wadda jaruma ce da ta shahara a masana’antar ta Kannywood sakamakon irin rawar da ta ke takawa wajen nishadantar da masu sha’awar kallon fina-finan Hausa.

“Komai da kuke gani lokaci ne ni macece mai farin jini Ina da masoya wadanda suke sona sama da biliyan daya” Inji Jarumar.

Wakilinmu ya rawaito cewar, jarumar wadda ta nishadantar da jama’a a wajen bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, ta ce idan lokaci ya yi za ta yi aure.

Leave a comment