Kwankwaso Mayaudari Ne, Mara Gaskiya – Ganduje

Daga Nasiru Salisu,Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje,ya bayyana cewa tun lokacin da suka Fara siyasa da Tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sanshi a matsayin Mayaudari ne mara gaskiya akan Harkokin siyasar sa.

Gwamna Ganduje,yace shine uban gidan Kwankwaso tun lokacin da suka Fara Harkokin siyasarsu, yana Mai cewa Duk kudin da Kwankwaso zai kashe a Harkokin siyasarsa lokacin mulkin soja shine yake daukar dawainiyar komai.
Ganduje ya bayyana haka ne yayin da yake karbar Tsohon Sakataran Gwamnatin jihar Kano Kuma Shugaban jami’iyyar PDP da ya Koma jami’iyyar APC Suleman Bichi da wasu mabiya jami’iyyar ta PDP a fadar Gwamnatin jihar.
Gwamnan ya ce” Tun lokacin da muka Fara siyasar mu Tare da Tsohon Shugaban Ku a zamanin soja Duk mun San cewa Mayaudari ne Kuma Mai kama karya Amma saboda a sauna lafiya muka barshi a ci gaba da tafiya har lokacin da Allah ya kawo mana karshensa a yanzu; Abu na biyu Shi kansa Tsohon jagoran naku bashi da kudi Duk lamarinsa a waccan lokacin Ni nakeyi Don lokuta da Dama zai Sani aiki amma bashi da kudin biya nine nake biya masa da aljihuna. Saboda haka Yanzu tabbata Kuma kun gano cewa Jagoranku da kukayi watsi da Shi Mayaudari ne” inji Ganduje.
A nasa jawabin Suleman Bichi, yace sun dawo jami’iyyar APC ne bisa bin umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ciyar da kasa gaba, a cewarsa, Shugaban Buhari yace Duk Wani Mai son ci gaba to ya shigo APC ayi aiki Tare da Shi.
” Mai girma Gwamna ka sanni Kuma Nima nasan ka Duk mun San irin badakalar da akayi a baya na son Rai, yanzu Ina Mai baka tabbacin cewa zamuyi aiki Tare; zamu baka Duk goyon bayan da suka kamata domin ciyar da jihar Kano gaba insha Allah” inji Bichi.
Bayan kammala jawabai ne Gwamna Ganduje ya jagoranci Kona jajayen huluna da wadanda sukayi bankwana da Darikar kwankwasiyya suka dawo APC.

Leave a comment